Google ya sayar da Motorola ga Lenovo

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanin Google ya sayar da kamfanin wayar salula na Amurka, Motorola Mobility ga kamfanin kwamfuta na China, Lenovo kan farashin $2.91 biliyan (N4.9 tiriliyan).

Kasa da shekaru biyu da su ka wuce dai Google ya sayi kamfanin kan $12.5 biliyan (N21.3 tiriliyan).

Lenovo na kokarin habaka sashensa na kera wayoyin komai-da-ruwanka ta hanyar sayen Motorola, wanda zai iya cike gibin da aka fara samu a cinikin kwamfuta.

Sai dai Google zai ci gaba da rike hakkin mallakar mafi yawan fasahohin da Motorola ya kirkira a baya, ciki har da manhajar Android.

A sanarwar da ya fitar, Google ya ce kasuwar wayoyin komai-da-ruwanka sai an yi da gaske, kuma Lenovo zai fi iya taimaka wa Motorola.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sayen Motorola dai ya mayar da Lenovo kamfanin wayar komai-da-ruwanka na uku a duniya bayan Samsung da Apple.

Kamfanin Strategy Analytics mai nazari kan kasuwar na'urorin sadarwa ya ce Lenovo zai amfana sosai da sayen Motorola.

Ya ce: "Lenovo zai samu kafar shiga kasuwar Amurka da kuma ta yankin Latin Amurka da ke ci gaba da bunkasa. Wannan zai fadada kasuwancin kwamfutocinsa.

"Ga Motorola kuma, zai samu wani uba mai kudi da ke da karfi a makekiyar kasuwar China. Shi Google ya rabu da kamfanin da ke jawo masa matukar asara."