Amurka ta damu a kan rashin mika makaman Syria masu guba

rusassun gine-gine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ko yaya za a shawo kan Syria ta ci gaba da mika makamanta?

Jami'an Amurka sun ce kasa da kashi biyar cikin dari na makaman ne kawai aka kwashe.

Duk wani yunkuri kuma na kwashe saura yana fuskantar tsaiko.

Sakataren tsaron Amurkar, Chuck Hagel, ya ce bai san dalilan da Syria ke da su ba na kasa cika alkawari, ko kuma tana da wasu matsaloli ne, ba a sani ba.

Mr Hagel ya ce zai yi magana da gwamnatin Rasha kan ta shiga wannan lamari.

Ya ce yawwa Amurka ta damu da yadda gwamnatin Syria ta ki mika makamanta masu guba akan lokaci bayan kuma yarjejeniyar da aka cimma da ita.

Ya ce ya yi magana da ministan tsaron Rasha kan su yi bakin kokarinsu dan tursasa wa gwamanatin Syria ta cika alkawari.