Ukraine ta yi wa masu bore afuwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar Ukrain ta yi afuwa ga masu bore da aka tsare

Majalisar dokokin Ukraine ta amince da kudurin dokar yin afuwa ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ake tsare da su wadanda suka shafe makwanni su na bore a kasar.

Jam'iyyun adawa dai sun ki amincewa da kudurin dokar da ta ce dole masu zanga-zangar su bar gine-ginen gwamnati da suka mamaye.

Tun da fari shugaba Vladimir Putin na Rasha a wani jawabi da ya yi wa 'yan majalisar zartarwarsa ya ce za a samu tsaiko wajen bada kudaden da kasar ta yi alkawari dan ceto Ukraine daga durkushewa.

Masu boren dai sun mamaye gine-gine da dama a babban birnin kasar, Kiev da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu .

Su na dai bukatar shugaba Victor Yanukovych ya yi murabus a kuma gudanar da sabon zabe.

Karin bayani