Wasu motoci a India ka iya ajalin mutum

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wajen kera motocin Tata a Nigeria

Wani bincike ya nuna cewa wasu daga cikin kananan motocin da ake kerawa a Indiya da suka fi farin jini na iya zama sanadiyar ajali ko haddasa mummunan rauni ga jama'a idan suka yi hadari.

An gano hakan ne sakamakon gwaji mai zaman kansa na farko da wata kungiya mai zaman kanta dake sa ido kan lafiyar motoci dake nan Birtaniya, mai suna, Global NCAP ta gudanar.

Daga cikin motocin da aka yi wa gwajin akwai Tana Nano, motar da ake cewa ita tafi kowace araha a duniya, da kuma wasu nau'o'in motocin kirar fitattun kampanoni na duniya irin su Ford da Volkswagen.

An yi gwajinne a kan wasu motoci iri daya wadanda ake sayar wa a India da kuma irinsu wadanda ake sayar wa a nahiyar Turai da kuma Amurka.