An kashe mutane 7 a kudancin Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jihar Kaduna na fama da rikicin kabilanci cikin 'yan shekarunan

A Jihar Kaduna dake arewacin Najeriya rahotanni na nuna cewa kimanin mutane 7 ne suka rasu, wasu kuma suka sami raunuka a wani rikici a kudancin jihar.

Sakamakon tashin hankalin dai an kona gidaje da masallatai a sabon garin Manchok dake karamar hukumar Kaura.

Wannan al'amari ya wakana ne yayin da wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suka kai hari cikin daren ranar Laraba inda suka hallaka mutane 7 'yan gida daya, daga bisani kuma hare-haren ramuwar gayya su ka biyo baya.

Yayin da kabilun yankin ke cewa Fulani ne suka kai harin fulanin na cewa ba su da wata masaniya.

Kudancin jahar kaduna dai na ci gaba da zama wani yanki da ake ta samun irin wannan hare-hare masu nasaba da addini da kabilanci.

Karin bayani