An gano Vodka na kashe mutane a Rasha

Barasa samfurin Vodka
Image caption An gano cewa yara na fara shan barasar ne tun daga shekarun kuruciya, abinda ke haddasa musu kawuwa da cututtukan da suka hada da sankarar hanta.

Wani bincike da aka gudanar a Rasha ya gano cewa kwankwadar barasa samfurin Vodka na hallaka kashi daya cikin hudu na maza a kasar da suke mutuwa kafin su kai shekaru 55.

Sabon rahoton da aka gudanar ya gano yadda yara 'yan sama da shekaru 10 su fiye da 150,000 ke shan barasar, abinda ke sanadiyyar mutuwarsu a cikin shekarun kuruciya a dalilin kamuwa da cututtukan da ake samu ta sanadiyyar gubar da ke cikin barasa, ko hatsari, ko tashin hankali ko su kashe kansu, ko kuma kamuwa da cutar makogwaro da sankarar hanta.

Binciken ya kuma bankado yawan mutuwar ya na matukar karuwa saboda tarurrukan siyasa.

An kuma gano bayan rushewar gwamnatin kwamunisanci a kasar Rasha da kuma rashin zaman lafiyar da ya biyo bayan hakan, mutane da dama na mutuwa sanadiyyar kwankwadar barasar.