An bukaci Syria ta mika ragowar makaman nukiliya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption za a sake zagaye na biyu kan tattaunawar sulhun a Syria

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun tattauna game da rashin ci gaban da aka samu kan sasanta bangarorin da ke rikici da juna a Syria.

Sun dai hadu ne a wani taro kan sha'anin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus, inda Mr Kerry ya bukaci takwaran nasa da ya matsawa gwamnatin Syria kan batun kwashe makamanta masu guba.

A taron da akai a Munich wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan sasanta rikicin Syria Lakhdar Brahimi ya amince cewa ba wani ci gaba da aka samu a taron da aka yi kan Syria.

Mr Brahimi da sauran abokan aikinsa sun nuna damuwarsu kan halin da al'ummar Syria ke ciki.

Shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch Kenneth Roth ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aiwatar da kudurinta domin bude iyakokin Syria dan a kai kayan Agaji ga mabukata.

Karin bayani