Dalilin shiga ta PDP - Shekarau

  • 1 Fabrairu 2014
Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau Image copyright Getty
Image caption Tsohon gwamnan ya koka ne da rashin adalci a jam'iyyar ta APC dalilin da ya sa ya ga gara ya fice daga cikinta.

A tsakiyar mako ne tsohon gwamnan jihar Kano Malama Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa Jam'iyyar PDP.

Malam Shekarau dai ya ce rashin adalci da shugabanci na gari shi ya sanya ya fice daga jam'iyyar duk kuwa da cewa su ne suka yanke mata cibi.

An dai fara samun rashin jituwa a jam'iyyar ne tun bayan shigowar gwamnonin nan biyar da suka fice daga jma'iyyar PDP suka dawo APC.

Malam shekarau ya koka kan cewa tun shigowarsu sai jam'iyyar ta fara tangal-tangal, ta fuskar nuna fifiko da ake nunawa tsakanin su da sauran wadanda suka tarar a cikin jam'iyyar, abinda ya kira da yin hakan rashin adalci ne.

Sai kuma batun rike shugabancin jam'iyya na tsahon watanni shida da tun da fari aka tsara, watanni uku na farko ayi rijistar 'yan jam'iyya da kuma kafa shugabannin riko a matakan kananan hukumomi da jiha, sai watanni uku na karshe za a yi zaben shugabanni a matakai daban-daban da babban taron jam'iyya na kasa amma har watanni shidan suka shude babu daya da aka yi daga cikin wadannan tsare-tsare.