'Yan bindiga sun kai hari a Madagali

'Yan bindiga sun sa ke kai hari a Karamar Hukumar Madagali dake Jihar Adamawan Najeriya inda su kashe wani pasto, su ka kuma tarwatsa jama'a.

A cikin mako daya dai an kashe fiye da mutane 40 a karamar hukumar a hare-haren da 'yan bindiga suka kai.

A harin baya baya nan, wanda aka kai a ranar Juma'a da daddare, 'yan bindigar sun shiga yankin ne da motoci da babura, su na sanye da kayan sojoji.

Shugaban karamar hukumar Madagalin, Maina Ularamu, ya gaya wa BBC cewa jama'ar yankin na zaune cikin fargaba sosai.

Ya ce mutane da dama sun gudu daga kauyuka sun koma garin Gulak domin samun mafaka.

Jihar Adamawa dai na daya daga cikin jihohi ukku a arewa-maso-gabacin Najeriya, wadanda aka sa wa dokar ta-baci domin magance matsalar tsaro. Sauran jihohin biyu sune Borno da Yobe.

Karin bayani