Morsi ya sake bayyana a kotu

Hakkin mallakar hoto AP

Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi ya bayyana a kotu yau a birnin Alkahira a cigaba da shari'ar da ake yi masa.

Morsin da kuma wasu 'yan Kungiyar 'Yan uwa Musulmi su 14 ana tuhumar sune da laifin ingiza jama'a suka kashe masu zanga zanga a gaban fadar shugaban kasa a shekara ta 2012.

Tsohon shugaban na fuskantar shari'u daban daban har huddu, kuma dukkansu su shafi zargin aikata manyan laifuka.

Shari'ar ta yau dai ta shafi zargin ingiza jama'a ne don kashe masu zanga zanga.

A wajen kotun, masu zanga zangar nuna goyon bayan gwamnati sun yi ta jifar motar lauyan dake kare Morsin domin hana shi shiga kotu. Amma dai ya samu damar shiga.

A bara ne sojoji suka hambarar da Mohammed Morsi bayan wani boren da jama'a suka yi a kasar.

Karin bayani