Za a ci gaba da shari'ar Morsi a Masar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mohammed Morsi zai sake fuskantar tuhuma

Nan gaba ne a yau Asabar za a ci gaba da daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi a birnin Alkhahira.

Ana zargin Mr Morsi da mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi 14 da laifin tunzura kisan masu zanga-zanga a wajen fadar shugaban kasa a shekarar 2012.

A zaman da kotu ta yi kwanaki hudu da suka gabata Mr Morsi ya yi ta ihu a kotun yana fadar cewa har yanzu shi ne halattaccen shugaban Masar.

An dai hambarar da gwamnatinsa a watan Yulin shekarar da ta gabata bayan gagarumin gangamin da aka yi a kasar na bukatar ya yi murabus.

A jiya juma'a 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga daruruwan magoya bayan Mr Morsi a biranen Alkhahira da Al-askandariyya da kuma Fanyoum.

Karin bayani