'Mutane sama da miliyan 3 na fuskantar yunwa a Sudan ta Kudu'

Masu gudun hijira a Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kimanin miliyan ukku da dubu dari bakwai ne ke matukar bukatar abinci a Sudan ta kudu.

Babban jami'i mai kula ayyukan agaji na majalisar a kasar yace rikin da ake yi ya kawo cikas a harkar kasuwanci.

Dubban mutane ne aka kashe a fadan da akeyi tsakanin dakarun gwamnati da sojojin 'yan tawayen da suka juwa masu baya.