Rasha ta samu sabani da Amurka kan Ukraine

'yan sanda a Kieve Hakkin mallakar hoto AP

Shugabannin Rasha da na kasashen yammacin duniya sun samu rashin jituwa akan makomar Ukraine a jawaban da suka yi a wani taron kasa-da-kasa akan tsaro a birnin Munich.

Sakataren tsaron Amurka John Kerry, yace Amurka da Tarayyar Turai, na tare da Jam'ar Ukraine, a yunkurin su na zabarwa kansu abokan tafiya.

Ukraine na cikin rikici tun watan Nuwanban da ya wuce lokacinda Shugaban kasar Victor Yanukovych ya gwammance ya rika dasawa da Russia a maimakon kulla kawance da Tarayyar Turai.