Najeriya- An kashe Sheik Adam Albani Zaria

Taswirar Jihar Kaduna Najeriya
Image caption Taswirar Jihar Kaduna Najeriya

A Najeriya a daren jiya ne wasu 'yan bindiga suka hallaka fitaccen malamin addinin Islaman nan Sheik Auwal Adam Albani Zaria tare da matarsa da dansa.

Kamar yadda shaidu suka bayyana 'yan bindigar sun harbe malamin da iyalin nasa ne lokacin da suke cikin mota suna kan hanyar su ta komawa gida daga makaranta a cikin garin Zaria jihar Kaduna.

Wadanda suka kai masa harin an bayyan cewa suna cikin wata mota ne kuma bayan da suka harbe shi da iyalin nasa sai da suka sake janyo shi daga cikin motar suka kara harbinsa don su tabbatar ya mutu.

Sai dai wasu rahotanni sun ce anan take ne dai uwargidan nasa ta rasu, amma malamin da dan nasa sai bayan an kai su asibitin Wusasa dake garin na Zaria ne rai ya yi halinsa.