Ana zabe a Thailad yayinda ake zanga-zanga

Masu bore a Thailand Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu bore don hana zabe a Thailand

Prime Ministar Thailand Yingluck Shinawat ta kada kuri'ar ta a babban zaben kasar da ake gudanarwa karkashin wasu tsauraran matakan tsaro da kuma boren da aka shafe watanni ana yi da nufin hana zaben.

Babbar jam'iyyar adawar kasar dai tana kaurace ma zaben, tana nuna bukatar maye gurbin gwamnatin da kwamitin wasu mutane da ba zababbu ba ne, wanda zai yaki cin hanci da rashawa.

Wani wakilin BBC a wata mazaba dake birnin Bangkok ya ce, gungu-gungu na masu zanga-zangar suna toshe kafar zaben ga masu yunkurin kada kuri'unsu.

Karin bayani