Ana gudanar da zabe a kasar Thailand

Zabe a kasar Thailand Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zabe a kasar Thailand

Prime Ministan Thailand Yingluck Shinawat ta kada kuri'ar ta a babban zaben kasar da ake gudanarwa karkashin wasu tsauraran matakan tsaro .

Babbar jam'iyar adawa kasar ta kauracewa zaben, yayin da magoya bayan ta ke ta yunkurin hana raba takardun kada kuri'ar a rumfunan zaben.

Ta bukaci da a maye gurbin gwamnatin da wani kwamiti na mutanen da da ba zababbu ba, da zai yaki cin hanci da rashawa.

Sa'oi kadan kafin fara kada kur'ar magoya bayan gwamnatin da masu adawa da ita sun yi wata arangama a Bangkok babban birnin kasar inda akalla mutane shida ne suka jikkata.

Wani wakilin BBC a wata mazaba dake birnin Bangkok ya ce, ya ga gungu-gungu na masu zanga-zangar suna toshe kafar zaben ga masu yunkurin kaada kuri'unsu, sai dai kuma a wasu yankunan an ba da rahoton cewa ana zaben cikin lumana.

Wannan zabe na gudana ne a wani yanayi da kasar ta Thailand ta samu wani matsanacin rarrabuwar kawuna, inda gardandamin da ake ba wai na ko shin wa zai ci galabar zaben ko akasin haka ba, amma a kan ko shin kan shi zaben zai gudana.