An bude filin jiragen saman Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai harin

Gwamnatin Nigeria ta ba da umarnin bude filin jiragen sama na Maiduguri da ke jihar Borno, watannin biyu bayan rufe shi.

An rufe filin ne bayan harin da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kai a wasu cibiyoin soji da kuma filin a watan Disambar da ta gabata.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta ce yanzu haka jirage na iya zirga-zirga a filin bayan an gyara na'urorin da suka lalace sanadiyar harin da aka kai wa filin.

Hukumar ta kara da cewa gwamnati ta sanya wasu na'urorin da za su rika sanya idanu kan abubuwan da ke faruwa a kan iyakar Nigeria da Kamaru

Karin bayani