Cin hanci ya yi katutu a Turai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cecilia Malmstrom na fatan za a yi gyara

Kwamishinar harkokin cikin gida ta Tarayyar Turai-EU ta yi gargadi game da irin girman matsalar cin hanci da rashawa a kasashe wakilan kungiyar, da ta ce ya yi katutu.

A lokacin da take gabatar da rahoton farko kan yaki da cin hanci a daukacin tarayyar Turan, Cecilia Malmstrom ta ce wannan matsala na sa ana yanke kauna da wasu cibiyoyi na dimokradiyya, yana kuma ba da kafa ga kungiyoyi na masu aikata miyagun laifukka.

Ta ce "Muna fatan wannan zai zamo mafarin daukar matakan gyara, da zai sa a dauki matakai na siyasa, da kuma dukkan abubuwan da suka dace a dukkan matakai, domin yakar cin hanci".

Kwamishinar ta ce, Tarayyar Turai na asarar sama da dala biliyan 160 a shekara, ga ayyukan cin hanci da rashawa, adadin da daidai yake da kasafin kudin tarayyar na shekara.

Karin bayani