Darajar kudin Ghana tana kara zubewa

'Yan kasar Ghana Hakkin mallakar hoto ATE
Image caption 'Yan kasar Ghana na kara fuskantar matsalolin rayuwa

A kasar Ghana ga alama faduwar da darajan kudin kasar wato Cedi yake ci gaba da yi a kowacce rana na barazana ga harakokin kasuwanci da kuma rayuwar al'ummar kasar ta yau da kullum.

Tuni dai 'yan kasuwar kasar suka fara kokawa kan yadda suka ce lamarin yake shafar harakokinsu.

Lamarin kuma na haddasa tsadar kayayyaki a cikin kasar tare da sanya rayuwar talakkawa cikin kunci.

Karin bayani