Sana'ar rini na fuskantar barazana a Kano

Image caption Ana rina kayayyaki ne a wadannan rijiyoyi sannan a shanya su a jikin bango

Sana'ar rini wacce ta yi fice a birnin Kano da ke Nigeria na fuskantar barazana sakamakon rashin tsaro da rashin kulawa. Wannan sana'a, wacce masu yin ta suka ce ta faro ne kusan shekaru 700, ta zamo ginshikin samun abinci ga masu yin ta.

Malam Haroun Baffa, daya daga cikin marina, ya shaidawa BBC cewa "na fara zuwa nan wajen ne tun ina karami, kuma ina jin dadin yadda nake taimakawa wajen gudanar da sana'a".

Ya ce ya yi gadon sana'ar ce daga iyayensa da kakaninsa wadanda suka kwashe shakaru aru-aru suna gudanar da ita.

Wani allo da aka kafa a marinar da ke Kofar Mata ya nuna cewa an fara sana'ar ne a shekarar "1498".

Image caption Haroun ya ce mutanen da ke sayan kayayyakin yanzu ba su da yawa

Rijiyoyin da ake zuba baba na da dama a wajen, kuma kowacce na dauke da baba mai dan yawa wacce za a rina kayayyaki da ita.

Ana tsoma kayayykin ne a cikin babar, kana su kwashe awowi kamar hudu domin a tabbatar sun runu kafin a fito da su.

Sai dai yawancin kayayyakin da ake yi iri daya ne.

'Rashin ciniki'

Birnin Kano dai shi ne cibiyar kasuwancin arewacin Nigeria, sai dai hare-haren da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kai a kansa ya sanya masu yawon bude idanu daga wasu sassan duniya sun dan ja da baya daga kai ziyara a birnin.

Image caption Masu rini a Kano na yin amfani da launi iri daya

Akasarin masu sayen kayan daga Nigeria na yin amfani da su lokacin bukukuwa.

Masu yawon bude idanu daga yammacin duniya suna sayen kayayyakin ne domin yin ado.

Malam Haroun ya ce, ''A baya muna da masu sayen kayayyakin kusan kodayaushe. Amma tun da aka fara kai hare-hare an bar mu da kayayyakin inda akan kwashe kimanin watanni shida kafin wani ya zo ya saya.

A cewarsa, fiye da rijiyoyin baba 100 sun daina aiki, yana mai cewa kasa da shara sun cika su.

Karin bayani