'Yan majalisar dokokin Kano sun koma APC

Image caption A karshen shekarar 2013 ne dai gwamna Kwankwaso da wasu gwamnonin Nigeria suka koma APC

'Yan majalisar dokokin jihar Kano da ke Nigeria guda 26 sun fice daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar zuwa APC.

'Yan majalisar dai sun ce sun koma APC ne saboda rashin amincewa da yadda PDP ke gudanar da al'amura.

Gaba dayan wadanda suka halarci zaman ne dai su 26 suka bayyana sauya shekar, yayin da sauran da ba su halarci zaman ba ciki kuwa har da shugaban majalisar ba su bayyana komawa APC din ba.

A karshen shekarar da ta gabata ne dai gwamnan jihar ta Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso tare da gwamnoni hudu na jam'iyyar PDP suka sauya sheka zuwa APC.

Akasarin 'yan majalisar dokokin tarayya daga jihar ta Kano sun fice daga PDP zuwa APC

Karin bayani