Mandela ya bar dala miliyan hudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da makarantu na cikin wadanda za su ci moriyar gadon Mandela

Marigayi Nelson Mandela ya bar rukunin gidajen da kimarsu ta kai dala miliyan hudu.

Masu kula da rabon gadon tsohon shugaban kasar ta Africa ta Kudu sun bayyana a cikin wasiyyar da ya bari cewa iyalansa za su raba fiye da dala dubu 100 da kuma wasu kudaden daga sayar da littattafansa.

Kazalika jam'iyyar ANC da masu yi wa Mandela aiki na musamman da makarantu da jami'oi za su samu wani kaso na dukiyar da ya bari.

Daya daga cikin masu rabon gabon, Dikgang Moseneke, ya ce babu wanda ya nuna rashin amincewa game da wasiyyar da Mista Mandela ya bari.

A baya dai an yi ce-ce-kuce tsakanin iyalan Mandela kan wanene daga cikinsu ya kamata ya yi gadon kaddarorinsa.

Mista Mandela ya mutu a watan Disamba yana da shekaru 95 a duniya.

Karin bayani