Boko Haram:Nigeria za ta sayo jiragen leken asiri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram dai ta hallaka dubban mutane musamman a arewacin Nigeria

Ministan harkokin gida na Nigeria, Abba Moro, ya ce gwamnatin kasar na shirin sayen jiragen sama na leken asiri uku don sanya ido a kan ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram.

A hira da manema labarai, Mista Moro, ya ce gwamnati za ta dauki matakin ne da zummar yakar ta'addanci da sauran manyan laifuka wadanda 'ya'yan kungiyar Boko Haram da haramtattun bakin haure ke yi a kasar.

Mista Moro ya ce, '' A ziyarar da na kai kwanakin baya zuwa Jamhuriyar Czech, mun je wuraren da ake sayar da jirage marasa matuka a Prague, kuma mun mika shawararwari ga hukumomin gwamnatin da lamarin ya shafa domin su sayi jirage uku. Da zarar mun samu amincewar yin hakan za mu sayo su''.

Sai dai Mista Moro bai bayyana adadin kudin da za su kashe wajen sayen jiragen ba, kuma bai fayyace ko an sanya su a cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2014 ba.

'Tsallakawa Kamaru'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jihar Borno na karkashin dokar ta-baci

Wani wakilin BBC ya ce Nigeria na kokarin tattaunawa da hukumomi a Kamaru don kulla yarjejeniya ta yadda dakarun Nigeria za su iya kai hari a sansanin 'yan Boko Haram a Kamarun.

Dubban mutane aka kashe tun bayan da aka soma yaki da 'yan Boko Haram shekaru biyar da suka wuce.

A kwanakin baya ne dai shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya kaddamar da wani jirgi mara matuki a Kaduna, sai dai wasu bayanai sun nuna cewa har yanzu bai fara aiki ba.

Amurka dai na amfani da jirage marasa matuka a kasashe irinsu Pakistan da Afghanistan domin zakulo 'yan ta'adda, sai dai sau da dama hare-haren da suke kai wa na fadawa kan fararen hula.

Karin bayani