An kama dan sandan da ya nemi cin hanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sandan Nigeria sun yi suna wajen cin hanci

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce ta kama dan sandan da aka dauki hoton bidiyonsa yana neman cin hanci na dalar Amurka a wajen wani mai mota.

Rundunar ta ce an fara gudanar da bincike kan dan sandan mai suna, Kofur Aniyem Chiyem, wanda ke aiki a karkashin yankin Isheri da ke jihar Lagos, kuma za a hukunta shi da zarar an same shi da laifi.

Kazalika rundunar ta ce Babban Sifeton 'yan sandan kasar, M.D. Abubakar, ya yabawa mutumin da ya dauki hoton bidiyon dan sandan.

Ya yi kira ga sauran 'yan kasar su dauki hoton bidiyon duk dan sandan da ya nemi su ba shi cin hanci.

Hoton bidiyon dai, wanda aka sanya a shafin Youtube, ya nuna dan sandan yana cewa ba zai karbi cin hanci da naira ba sai da dalar Amurka.

Karin bayani