'Yan Saudiyya za su sha daurin shekaru 20

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ta ce za a hukunta duk dan kasar da aka gano yana hulda da 'yan ta'adda

Wata sabuwar doka da gwamnatin Saudi Arabia ta kaddamar ta ce duk dan kasar da aka gano ya shiga yakin da ake yi a Syria ko wasu kasashen zai sha daurin shekaru uku zuwa shekaru 20 a gidan yari.

'Yan kasar ta Saudiyya da dama ne dai suka shiga cikin 'yan adawar da ke yaki da shugaba Assad na Syria.

Ita kanta gwamnatin kasar tana goyon bayan wasu 'yan adawar na Syria.

Sai dai tana fargabar cewa 'yan kasar nata za su iya koyo tsattsauran ra'ayin addini, sannan su dawo kasar domin yi mata bore.

Dokar ta kara da cewa za a hukunta duk dan kasar da ya shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Karin bayani