APC: Me komawar Atiku za ta haifar ?

Image caption Atiku Abubakar ya bukaci magoya bayansa su yi rijista a APC

Tun bayan da tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC daga jam'iyyar PDP da aka kafa tare da shi, aka soma tsokaci a kan yadda hakan ka iya tasiri ga makomar jam'iyyar mai mulkin kasar.

Masu sharhi na kallon, Atiku Abubakar a matsayin dan siyasa wanda ke da dumbin magoya baya musamman saboda yanayinsa na 'sakin hannu' ga mutane.

A wata sanarwa da ya fitar, Atiku Abubakar ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne bayan tattaunawa sosai da magoya bayansa game da tayin da shugabannin APC suka yi masa na shiga jam'iyyar.

Dunkulewar 'yan adawa a jam'iyyar APC wata babbar barazana ce ga PDP, kuma wasu na ganin cewar zaben 2015 zai kasance mafi sarkakiya tun bayan komawar kasar mulkin demokradiyar a shekarar 1999.

Alhaji Atiku Abubakar, ya zama na baya bayan nan da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai jan ragamar mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC, bayan da a 'yan watannin baya wasu gwamnoni biyar suma suka yi hakan.

'Kawancen Arewa da Yammacin Nigeria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'iyyar adawa ta APC na zawarcin Obasanjo

A tarihin siyasar Nigeria duk lokacin da yankin arewacin kasar ya kulla kawance da yankin yammacin kasar (kabilar yarabawa), ana kallon matakin a matsayin abinda zai yi matukar tasiri a lokacin zabuka.

Arewacin Nigeria da yankin kudu maso yammacin kasar su ne suka fi kowanne yanki yawan masu kada kuri'a kuma duk inda suka dosa indai baki ya zo daya , tabbas akwai kallo sosai a rumfunan zabe.

Shi dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya kuma bukaci magoya bayansa da su gaggauta yin rijistar shiga jam'iyyar APC da zarar an fara domin ceto Najeriyar daga halin da suka ce ta fada.

Ya bayyana takaicinsa game da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP da suka kafa, inda ya ce hakan ya sa shi da wasu jiga-jiganta suka fice daga babban taron jam'iyyar da aka gudanar a Abuja a shekarar daga gabata.

Yanzu haka dai jam'iyyar adawa ta APC ta samu karin gwamnoni biyar da kuma sanatoci da 'yan majalisar wakilai wadanda suka balle daga PDP.

A daidai lokacin da ake dosar zabukan 2015, bisa dukkan alamu karin tagomashin APC musamman a arewacin Nigeria na nuna alamun cewar jam'iyyar za ta iya bada mamaki idan har ta iya warware wasu matsaloli na cikin gida da ke kunno kai.

Karin bayani