Duniya ta ji kunya kan Syria - Italiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kasa cimma matsaya a taron sulhu kan Syria

Ministar harkokin wajen Italiya, Emma Bonino ta ce duniya ta ji kunya kan yadda ta gaza raba kayan agaji a Syria.

A lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya a Roma, Ms Bonino ta ce duk da cewar rikicin Syria shi ne ya fi jefa jama'a cikin mawuyacin hali a 'yan shekarun nan, akwai isassun kayan agaji da ya kamata a taimaka ma wadanda aka rutsa da su a fadan.

Ta ce "Ya zama wajibi mu amsa cewar, al'umar duniya ta gaza wajen ganin abincin agaji ya isa wuraren da ake bukata a Syria".

Kawai dai ba a kai wa mutanen ba ne.

An yi taron ne da nufin duba hanyoyin da za a yi matsin lamba kan gwamnatin Syria da kuma 'yan adawa domin ganin sun kulla wani abin azo-agani, idan suka koma shawarwari nan gaba a wannan wata.

Karin bayani