Shari'a kan kisan kare dangi a Rwanda

Wajen Kotun a birnin Paris, kasar Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wajen Kotun a birnin Paris, kasar Faransa

Za a fara sauraron kara kan kisan kare dangi a Paris babban birnin kasar Faransa, wanda ya faru a kasar Rwanda shekaru 20 da suka gabata.

Tsohon jami'in hukumar leken asirin kasar Rwanda Pascal Simbikangwa da ake tuhuma da laifin kitsa kisan kare dangin da aka hallaka dubun dubatar mutane zai bayyana a kotu a karon farko.

Masu suka sun ce a cikin shekaru da dama gwamnatocin Faransar da suka shude sun yi ta dakatar da duk wani yunkuri na bankadowa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Alain Ngirinshuti wani wanda ya tsira daga kisan kare dangin, kuma mataimakin shugaban wata kungiya mai zaman kanta dake tallafawa wadanda lamarin ya rutsa da su mai suna Ibuka France na cikin wadanda za su bayyana a kotun.

Clemence Bectarte lauya a wata kungiyar kare hakkin biladama ta kasa da kasa, daya daga cikin kungiyoyin dake bin diddigin karar ta ce akwai nuna halin ko in kula daga mahukuntan kasar Faransa wajen shigar da karar game da lamarin.