Ana tashin hankali a garin Kankia na Katsina

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tura jami'an tsaron don kwantar da hankali

Rahotanni daga garin Kankia a Jihar Katsina na Nigeria na cewar an yi wata zanga zanga yau a garin, wadda ta kai ga kone konen wasu gidaje a garin.

Zanga zangar ta biyo bayan gawar wata yarinya ce da aka gano a wani gida.

Baya ga kone-konen tayoyi a kan babbar hanyar da ratsa garin na Kankia an kuma ce an kona wasu gidaje a wata unguwa da ake kira sabuwar Abuja.

Malam Kabiru Daurawa, wani mai hidimar Kasa a Kankia ya ce an kwashesu zuwa wani caji ofis don kada matasa su farmusu.

Dan majalisar wakilai dake wakiltar yankin, Ahmed Babba Kaita ya shaidawa BBC cewar bayanan da ya samu sun nuna cewar an soma tashin hankalin ne sakamakon ganin gawar wata yarinya a gidan wani mutumi kirista inda aka cire mata wasu sassan jikinta.

An tura jami'an tsaro don magance rikicin.

Karin bayani