Bill Gates ya sauka daga mukaminsa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mista Gates ya ce babu wani mutum da ya fi Mista Nadella cancanta ya shugabanci kamfanin.

Kamfanin Microsoft ya ce Bill Gates zai sauka daga mukaminsa na jagorancinsa, amma zai zama mai ba da shawara kan fasaha na kamfanin.

Bill Gates ne dai ya kafa kamfanin na Microsoft.

Kazalika, kamfanin ya nada Satya Nadella sabon shugabansa.

Mista Nadella, wanda aka haifa a kasar India, zai zama shugaba na uku a tarihin Microsoft, inda zai maye gurbin Steve Ballmer.

Mista Gates ya ce babu wani mutum da ya fi Mista Nadella cancanta ya shugabanci kamfanin a wannan lokaci da a cewarsa, ake samun sauye-sauye a fasahar sadarwa.

Karin bayani