An kashe mutane fiye da 20 a Filato

Hare-hare a Najeriya Hakkin mallakar hoto v
Image caption Hare-hare a Najeriya

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa an kashe mutane fiye da ashirin cikinsu har da jami'an tsaro a wani hari da aka kai kan wasu kauyuka a karamar hukumar Riyom.

Hukumomi dai sun bayyana cewa suna yi wa wasu sarakunan gargajiya da lamarin da ya faru a yankunansu, tambayoyi.

Rahotanni sun ce maharan wadanda ba a tabbatar da ko su wane ne ba, sun kai harin ne a kauyukan Atakar da kuma Dajat dake cikin karamar hukumar ta Riyom jiya da asuba, sun kuma yi amfani da bindigogi wajen afka wa mutanen kauyukan.

Kakakin rundunar 'yan-sandan jihar ta Filato DSP Fellicia Anslem, ta shaidawa BBC cewa maharan sun zo ne suka kona wasu gidaje masu jinkar ciyawa, kana suka kashe mutane da suka hada da farar hula 19 da kuma jamiā€™an tsaro biyu.

Mutane da dama ne suka tsere wa gidajensu a kauyukan dake yankin da aka kai wa harin.