An haramta gangamin siyasa a Rivers

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Ameachi

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers dake kudancin Nigeria ta haramta gangamin siyasa a cikin jihar.

Rundunar ta ce ta dauki matakinne saboda yadda harkokin siyasar jihar su ka yi zafi.

Ana kallon haramcin a matsayin wata hanya ta takurawa magoya bayan gwamnan jihar, Rotimi Ameachi wanda ke takun saka da kwamishinan 'yan sanda jihar, Mr Joseph Mbu.

Magoya bayan gwamnan sun ce kwamishinan 'yan sandan baida hurumin dakatar da gangamin siyasa a bisa tsarin dokar kasar.

Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Ameachi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC bayan takun sakar sa da wasu daga cikin 'yan koran Shugaba Goodluck Jonathan.

Karin bayani