Gobara ta kona shaguna 200 a Sokoto

Image caption Ana yawan samun gobara a kasuwannin Nigeria

Dukiya ta miliyoyin naira ta salwanta sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar kara dake jihar Sokoto a arewacin Nigeria.

Gobarar wacce ta tashi a daren ranar Talata ta kona shaguna fiye da 200.

Kasuwar ta yi fice wajen sayar da hatsi da kayayyakin amfani yau da kullum.

Rahotanni sun nuna cewar gobarar ta tashi ne sakamakon toci na wutan lantarki.

Babu wanda aka bada rahoton ya rasu sakamakon gobarar.

Karin bayani