Murna game da lalata makaman Libya

Makamai masui guba na kasar Libya Hakkin mallakar hoto .
Image caption Makamai masui guba na kasar Libya

Hukumar sa ido kan lalata makamai masu guba ta kasa da kasa ta yi na'am da sanarwar da Libya ta bayar kan lalata makamanta masu guba.

Ministan harkokin wajen na Libya Mohammad Abdul-Aziz ya ce sun lalata akasarin makamanta masu hadarin gaske kamar su bama-bamai da iska mai guba tun karshen watan da ya gabata da taimakon kasashen waje.

An dai jinjinawa wannan mataki a matsayin wani misali ga kasar Syria wadda ya kamata ace zuwa yau din nan ta kammala yin waje da makaman na ta masu guba.

Wannan mataki dai ya fara ne tun a shekara ta 2004 a karkashin jagorancin marigayi shugabana kasar ta Libya Kanal Gaddafi, lokacin da kasar ta ayyana ajiyayyun tan 13 na iskar mai guba hukumar sa ido kan shirin lalata makamai masu guba ta kasa da kasa.

Kasar Rasha dai ta ce ta samu tabbaci daga gwamnatin Syriar cewa, za a kammala na ta shirin na lalata makamai masu gubar daga nan zuwa farkon watan Maris.