'An bukaci a soke zaben kasar Thailand'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan adawa sun kauracewa zaben

Babbar jam'iyyar adawa ta Thailand, Democrat Party, ta yi kira ga kotun tsarin mulki ta kasar, da ta soke babban zaben kasar da aka yi ta kawo cikas lokacin gudanar da shi.

Lauyan jam'iyyar Wiratana Kalayasiri ya ce "Dalili shi ne, manufar zabe ita ce ya kamata ace dukkan 'yan kasa sun shiga cikinsa. Do haka ya dace a kwatanta adalci wajen gudanar da shi".

Lauyan ya kuma ce, takardar koken ta yi kira da a haramta jam'iyya mai mulki ta Firaminista Yingluck Shinawatra.

Ita dai jam'iyyar Democrat ta kaurace wa zaben ne, yayinda masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati suka rika kange hanyoyin zuwa rumfunan zabe a Bangkok da kuma a kudancin kasar ta Thailand, lamarin da ya hana miliyoyin jama'a yin zaben.

Masu zanga-zangar na so ne firaministar ta sauka, a kuma yi wa tsarin siyasar kasar kwaskwarima.