Jagoran Sojin Masar Al sisi zai fito takara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al sisi na Masar zai fito takarar shugabancin kasar

Jaridar kasar Kuwait ta rawaito cewa shugaban rundunar sojin kasar Masar Abdel Fatta al-Sisi na cewa zai tsaya takarar shugaban kasa.

Jaridar Al Seeyassah ta ambato Field Mashar Sisi na cewa ba bu yadda zai yi baya ga ya amince da bukatar Misrawa na fitowa takarar shugaban kasar.

An dai dade ana jiran ya bayyana matsayinsa game da hakan, sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Sojojin Masar.

Al-Sisi farin jininsa ya ragu bayan jagorantar juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin shugaba Mohammad Morsi a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Masu suka lamari dai na ganin cewa in har aka zabe shi to Masar za ta sake komawa karkashin mulkin soja, shekaru uku bayan juyin-juya halin da ya hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak da shi ma ya kasance Soja.

Karin bayani