A Najeriya APC ta fara rijista

Image caption APC na yin rijistar 'ya'yanta

A Nigeria, sabuwar jam'iyyar hamayya ta hadaka wato APC ta fara rijistar 'ya'yan ta a duk fadin kasar.

Yankar katin zai ba wadanda suka samu katin damar zaba ko a zabe su a mukaman jam'iyyar.

Kwanaki biyar ne dai jam'iyyar ta tsara za a yi ana yin rijistar masu sha'awar shiga jam'iyyar, inda a kowane akwatu za a yi wa mutane 100 rijistar.

An fara yin rijistar a wasu sassa na Jihar Kano sai dai akwai inda ba a fara rijistar ba.

Karin bayani