'Kada ku bamu kunya a kan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kafa dokar ta-baci don murkushe 'yan Boko Haram

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya bukaci shugabannin dakarun kasar kada su bada kunya wajen kokarin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Ya shaidawa jami'an tsaron a Abuja cewar "dole ne kasar ta samu nasara a kan yaki da ta'addanci saboda kada su kunyata 'yan Nigeria".

A cikin watan Junairu ne Shugaba Jonathan ya kori manyan hafsoshin dakarun kasar, ya maye gurbinsu da wasu sabobbi, kwanaki biyu bayan da wani bam ya kashe mutane 19 a Maiduguri.

Sabon babban hafsan dakarun Nigeria, Air Marshal Alex Badeh ya bayyana aniyar jami'an tsaron kasar ta kawo karshen zubar da jinin da ake yi sakamakon ayyukan 'yan Boko Haram.

Daruruwan mutane ne suka mutu rikicin da ake yi tsakanin Boko Haram da jami'an tsaron kasar.

Tun a watan Mayun 2013, Shugaba Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa a kokarin samun zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Karin bayani