Gwamna a Kenya ya janye kalamansa kan mata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnan ya ce idan har mace ba za ta iya tafiyar da al'amuran gida ba, ba za ta iya gudanar da harkokin jama'a ba.

Wani gwamna a kasar Kenya ya ba da hakuri saboda kalaman da ya yi cewa bai kamata matan da ba su da aure su shiga harkokin siyasa ba.

Mista William Kabogo dai ya ce idan har mace ta kai shekaru 35 ba ta yi aure ba, to lallai akwai abin da ke damunta.

Ya kara da cewa idan har mace ba za ta iya tafiyar da al'amuran gida ba, ba za ta iya gudanar da harkokin jama'a ba.

Ya yi kalaman ne saboda wata 'yar majalisar dokoki da ba ta da aure mai suna Alice Ng'ang'a, wacce ke adawa da shirinsa na sanya sabon haraji a jihar.

Wasu kungiyoyin mata sun zargi gwamnan da nuna bambanci, suna masu cewa ba ruwan mulki da jinsi, illa dai basira ake nema.

Karin bayani