A daina bayyana manufofin kasa a wuraren Ibada

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

Malaman addinai a Najeriya sun fara kokawa kan yadda wasu shuwagabanni na syasa kan yi amfani da wuraren ibada wajen bada sanarwar wasu muhimman manufoifi na gwamnati ko shirye-shirye na siyasa a maimakon su rika yin hakan a gidan gwamnati ko a tarukan siyasa ko na jama'a.

Najeriya dai kasa ce da addinan Islama da na kirista ke da karfi matuka amma a kan ga shuwagabanni na siyasa kan gabatar da manufofi na gwamnati a wajen ibadar addininsu duk da cewa kasar kusan a dukkan matai ta kunshi mabiya addinai daban-daban.

Babban Bishop na Katholika na yankin Jos, kuma Shugaban Bishop-Bishop na Nijeriya, Most Reverend Ignicious Kaigama, ya bayyana cewa wuraren Ibada, ba wurare ba ne da bayyana manufofin kasa.

Ya yi kira ga Ministoci da Gwamnoni da Shugaban kasa, su daina yin haka, yana cewa idan wani abu ne da ya shafi ilimi a je Makaranta a fada.

Karin bayani