Caremark zai daina sayar da sigari a Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obama ya ce matakin zai taimakawa 'yan kasar su daina shan sigari

Daya daga cikin manyan kamfanonin sayar da magunguna a Amurka, CVS Caremark, ya ce zai daina sayar da taba sigari daga watan Oktoba mai zuwa.

Shugaban kamfanin, Larry Merlo, ya ce taba ba ta da hurumi a cikin harkokin kiwon lafiya.

Kamfanin ya ce wannan mataki zai sa su yi asarar kusan dala biliyan biyu na kudin da suke samu duk shekara, sai dai kuma, a cewarsa, za su mayar da ribar ta wasu bangarorin.

Shugaba Barack Obama ya ce matakin zai inganta kiwon lafiya a kasar.

Ya taya kamfanin murna game da abin da ya ce yunkuri ne da zai taimaka wa miliyoyin 'yan kasar su daina shan taba

Karin bayani