Vatican ta maida martani ga majalisar dinkin duniya

Hakkin mallakar hoto NA

Fadar Paparoma ta Vatican ta yi kakkausar suka kan wani rahoto na majalisar dinkin duniya dake zarginta da amfani da wasu manufofi da suka kyale malaman cocin suna yin fyade.

Lamarin dai ya shafi dubban kananan yara ne a wasu sassan duniya.

Wani kwamitin majalisar dinkin duniya ya ce ya zama wajibi Cocin Roman Katolika ya kori dukkan wasu sanannun masu cin zarafin yara kanana.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma bukaci fadar Vatican ta mika wadanda ake zargi ga hukumomi.

Jakadan Vatican a majalisar dinkin duniyar, Archibishop Silvano Maria Tomasi ya ce rahoton bai musu adalci ba.