'Masar: Al-Sisi ba zai tsaya takara ba'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun ce rahoton tsayawa takarar al-Sisi ba shi da tushe

Rundunar sojin Masar ta musanta rahoton da wata jaridar Kuwaiti ta buga cewa shugaban rundunar, Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi, zai yi takarar shugabancin kasar.

Jaridar, mai suna al-Seeyassah, ta ambato Field Marshal al-Sisi yana cewa ba shi da zabin da ya wuce tsayawa takarar shugabancin kasar saboda kiraye-kirayen da jama'ar kasar ke yi masa domin ya yi hakan.

Sai dai a wata sanarwa da gwamnatin kasar ta wallafa a shafin intanet, kakakinta ya ce a rahoton jaridar babu kanshin gaskiya.

Ya kara da cewa idan har al-Sisi zai tsaya takara, zai yi haka ne a gaban 'yan kasar ta Masar.

An yi ammanar cewa Field Marshall al-Sisi ne ke kan gaba a lokacin da aka hambare shugaban kasar mai kishin islama, Mohamed Morsi, daga mulki a bara.

Karin bayani