IBM ya fara samar da kwamfyutoci a Africa

Image caption Kamfanin ya ce matakin zai kawo bunkasar tattalin arzikin Africa

Katafaren kamfanin IBM da ke yin kwafyuta ya fara samar da na'urorin kwafyuta ga sassa daban-daban na Africa.

Manufar wannan shiri dai ita ce taimaka wa nahiyar domin fuskantar kalubalen da take fama da shi a fannin kiwon lafiya da tattalin arziki da noma.

IBM, wanda shi ne kamfanin da ya fi girma a harkar kwafyuta a duniya, ya ce zai kashe $100m, sannan za a dauki shekaru goma ana gudanar da shi a nahiyar, musamman a gabashin Africa.

Shugaban kamfanin, Ginni Rometty, ya shaidawa mahalarta wani taro ranar Laraba cewa akwai bukatar amfani da fasaha domin bunkasa aikin gona, yana ba da misali da kasar Morocco wacce ke amfani da fasaha wajen hasashen yanayi da inganta irin shuka da kuma yin rigakafin aukuwar cututtukan tsirrai.

Karin bayani