India ta gindaya sharuda kan 'yan Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption India ta ce ba za ta bai wa 'yan kasashe takwas wannan dama ba saboda dalilai na tsaro

Kasar India ta sassauta wa masu yawon bude ido daga kasashe 180 hanyar da suke bi don samun takardar shiga kasar, sai dai Nigeria na cikin kasashen da ba su samu wannan sassauci ba saboda dalilai na tsaro.

A halin da ake ciki dai, akasarin 'yan kasashen waje na jira tsawon makonni da dama kafin a ba su takardar izinin shiga India bayan sun bukaci yin hakan a ofisoshin da ke amincewa a shiga kasar.

Sai dai a karkashin sabon tsarin, wanda zai fara aiki a cikin wannan shekarar, masu son shiga kasar za su nemi izini ne ta hanyar intanet, sannan za a shaida musu idan an amince da bukatarsu cikin makonni biyar.

Hukumomin kasar ta India dai sun ce ba za su bai wa 'yan kasashe takwas wannan dama ba saboda kalubalen tsaron da ake fuskanta a kasashen.

Kasashen su ne Nigeria, Afghanistan, Iran, Iraq,Pakistan, Somalia, Sri Lanka da Sudan .

Karin bayani