Shirin Sure-P bai cimma gaci ba a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shirin Sure-P ya gaza cimma buri a Najeriya

A Najeriya shirin gwamnatin Tarayya na rage radadin janye tallafin man fetur wato Sure-P bai cimma gaci ba.

Kimanin shekaru biyu da suka wuce ne gwamnatin Nigeria ta kirkiro wata hukuma ta rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

Wasu ayyuka na musamman ne dai aka tsara hukumar ta Sure-P za ta yi a duka fadin kasar, wadan da suka hada da samar da ayyukan yi ga dubban matsan kasar, da kuma gyaran hanyoyi.

To sai dai daya daga daga manyan jami'an hukumar ya ce ya ajiye aiki da hukumar, inda yace dukkan alamu sun tabbatar masa ba za a cimma manufar kafa hukumar ba.

Karin bayani