Jami'ar diplomasiyyar Amurka ta nemi afuwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nuland ta nemi afuwa kan tsegumi da suka yi

Wata babbar jami'ar Diplomasiyyar Amurka ta nemi afuwa bayan bayyanar wata muryarta da aka nada inda a ciki ta muzanta Kungiyar Tarayyar Turai kan rawar Kungiyar ta taka a Ukraine.

Amurka dai ta nuna cewa Rasha ce ta nadi muryar Miss Victoria Nuland ta kuma kwarmata, inda ta bayyana cewa wannan wani sabon salon nuna rashin sanin ya kamata ne a yadda Rasha ke gudanar da ayyukanta.

Ma'iakatar harkokin wajen Amurka ta ce mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Victoria Nuland ta kira abokan aikin ta na tarayyar turai ta nemi afuwarsu kuma bata musanta ingancin muryarta da aka nada ba.

Haka ma dai mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki a bayanin da tayi ta tabbatar da ingancin hirar da aka nada yayin da ta ce Ms Nuland ta nemi afuwa ga Kungiyar Tarayyar Turai.

Karin bayani