Dambarwar kasafin kudin Najeriya

Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministar ta ce matakin da 'yan majalisar suka dauka bai da me ta.

Ministar kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta kwatanta dakatar da muhawara a kan kasafin kudi na bana a Majalisar Wakilan kasar da yunkurin da masu ra'ayin rikau na jam'iyyar Republican suka yi na hana cimma yarjejeniya a kan kasafin kudi bara.

A wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Mrs Okonjo-Iweala ta kuma ce wannan lamari bai dame ta ba.

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan majalisar wakilan daga jam'iyyar adawa ta APC suka bukaci a dakatar da muhawara a kan kasafin.

Sai dai kuma wasu na ganin wannan wata dabara ce ta aiwatar da umarnin jam'iyyar APC na hana muhawara a kan duk wani kuduri da shugaban kasa ya gabatar har sai an warware rikita-rikitar siyasar da ta dabaibaye Jihar Rivers wacce ke kudu maso kudancin kasar.

Karin bayani