Dan Nigeria ya zama alkalin alkalan Gambia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Yahya Jammeh na Gambia

Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya nada wani dan Nigeria Emmanuel Fagbenle a matsayin babban alkalin alkalan kasar.

Mai shari'a Fagbenle wanda zai rike mukamin a matsayin babban jojin riko, ya maye gurbin 'yar Ghana Mabel Yamoa Agyemang wanda aka sallameta daga mukamin ba tare da bada cikakkun bayanai.

Sanarwa daga fadar shugaban kasar, ba ta bada karin haske ba game da tarihin sabon babban jojin kasar.

Ita dai Agyemang wacce aka cire a yanzu, ta maye gurbin wani dan Nigeria ne Joseph Wowo wanda a watan Yulin bara ya rasa mukaminsa saboda wasu batutuwan da suka shafi zargin cin hanci da rashawa.

Shugaba Jammeh ya hau kan mulki ne tun a shekarar 1994 a Gambia kuma a shekara ta 2012 aka ranstar da shi a karo na hudu.

Karin bayani