INEC ta ce babu zabe da komfuta a 2015

Image caption Shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben ta Nigeria-INEC ta bayyana cewar ba za ta iya amfani da tsarin zabe mai amfani da na'ura mai kwakwalwa ba da ake kira e-voting a zabukan shekara ta 2015.

Kakakin INEC, Nick Dazang ya shaidawa BBC cewar dokar zaben kasar ba ta bada damar gudanar da zabe da na'ura mai kwakwalwa ba.

Sannan kuma a cewarsa " idan har aka bada damar a yi zaben da komputa, lokaci ya kure da INEC za ta iya amfani da wadannan na'urorin".

Shi dai irin wannan tsari wanda ake amfani da shi a kasashe kamar India, ya na rage tsawon lokacin da jama'a ke shafewa wajen kada kuri'a da saukin kidaya da kuma rage magudin kuri'a a lokacin zabe.

Wasu 'yan siyasa dai musamman ma 'yan adawa sun yi ta kiran da a bullo da irin wannan tsari tun bayan zaben shekara ta 2011.

Karin bayani